Labarai

Tinubu Zai Samar Da Tabarau Miliyan Biyar Ga Masu Fama Da Ciwon Ido

 

Ranar Juma’a ta makon da ya gabata ne a Abuja Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tsarin tallafa wa masu fama da matsalar ido, wanda hadin gwiwa ne tsakanin ma’aikatar lafiya ta tarayya da shirin tsarin lafiyar idanu ta kasa, wato gidauniyar, ‘Peek Bision’ wajen samar wa ‘yan Nijeriya fiye da miliyan biyar da suke fama da matsalar rashin gani sosai Tabarau wanda za su rika amfani da shi.

Shugaban ya tuna da yadda a karo na farko ya taba taimakawa na kusa da shi kan al’amarin da ya shafi lafiyar idanu, wannan ya say a dauki alkawari a madadin gwamnatin tarayya lokacin da aka kai ma shi ziyarar ban girma da jagora kuma shugaban gidauniyar ‘Peek Bision’, har ila yau tare da shi aka kafa gidauniyar  kulawa ta gani,Andrew Bastawrous.

Ya ce “Abu na farko shi ne dangane da wannan al’amari shi ne mahaifiyata Allah ya jikanta, bata lafiyar idanu hakan ne yasa bata iya gane ko wanene ni, amma dana samar mata da taimako aka kula da ita wajen ba da magani da bata Tabarau. Tambayar da ta yi mani ita ce kai nawa ne kai mani wannan abin alhairi, yanzu ya za ayi da mata da yara wadanda basu da wadanda za su  taimaka masu?.

“Sai na yi mata alkawarin zan taimaka wa mutane da yawa ta hanyar kulawa da lafiyar idanunsu ba da wasa ba, shi taimakon kulawa da lafiyar ido kyauta ne tare da yin gwaji da kuma tiyata, saboda tambayar da mahaifiyata ta yi mani da sha’awarta ta a taimakawa wajen raba wasu da cutar.

Daga karshe mun taimaka wa lafiyar idanun miliyoyin mutane a Legas za kuma za a iya lura da hakan wajen farin ciki da annashuwar da su ke ciki, domin an kara inganta masu al’amarin ganinsu ta hanyar basu Tabarau, kamar yadda Shugaban yace.

Da yake kara jaddada muhimmancin kulawa da inganta kulawa da lafiyar idanu a Nijeriya Shugaban kasa Tinubu ya nuna damuwarsa inda ya ce fiye da mutane milyan 24 suna fama da matsalolin da suka shafi idanu daban-daban.

“Lokaci ya yi wanda za mu dauki mataki saboda ai maganar gani da ji ba a wasa da al’amarinsu ba, saboda suna taka muhimmiyar wajen bunkasa tattalin arziki kamar yadda Shugaban ya ce,da  ya tuna  da wani  tsarin kula da lafiya wanda ya aiwatar  mai suna tsarin “Jigi Bola”, wanda  aka aiwatar lokacin da yake wa’adinsa na farko a matsayinsa na gwamnan Jihar Legas a shekarar 2001 inda aka kula da lafiyar idanun mutane kyauta na al’ummar Legas, inda aka  bude sabon babi na kula da lafiyar al’umma a Afirka ta yamma.

Jaridar Leadership

Leave a Reply