Latest:
Labarai

Ƴan gudun hijira 10,000 ne suka tsere daga Sudan zuwa Sudan ta Kudu

Sama da mutane 10,000 ne suka yi rajistar zama ‘yan gudun hijira a Sudan ta Kudu bayan da suka tsere daga rikicin Sudan, in ji ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD Ocha.

Yayin da baki daya, mutane 130,000 suka tsere zuwa Sudan ta Kudu tun bayan barkewar fadan a watan Afrilu, yawancinsu ‘yan Sudan ta Kudu ne da ke komawa gida.

Ocha ya ce ‘yan gudun hijira na baya-bayan nan na ci gaba da tabarbarewar al’amura yayin da ake hasashen adadinsu zai ci gaba da karuwa yayin da ake ci gaba da gwabza fada.

Ocha ya kara da cewa daga cikin wadanda suka isa wurin sun haɗa da yaran da suka rabu da ƴan uwan su, tsofaffi, nakasassu, masu buƙatar jinya na gaggawa, mata da sune masu riƙe gida da kuma mata masu juna biyu.

Yawancin baƙin da suka iso sun hadu da tashe-tashen hankula da cin zarafi kamar kwace da wawure dukiyar kasa, ciki har da lokacin da suke tafiya Sudan ta Kudu.

Idan aka yi la’akari da sauran makwabtan Sudan, Masar – mai 255,000 – da Chadi – mai 120,000 – sun dauki mafi yawan ‘yan gudun hijirar da ke tserewa daga tashin hankali.

BBC Hausa

Leave a Reply