Latest:
Labarai

Harin Bam Ya Kashe Mutum 21 A Kabul

‘Yan sanda a Kabul babban birnin Afghanistan sun ce harin bam da aka kai wani masallaci mai cunkoson jama’a ya yi sanadin mutuwar mutum 21.

Mai magana da yawun ‘yan sandan, Khalid Zadran, ya ce akwai wasu mutum 33 da suka samu raunuka a harin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da ake sallar magriba a ranar Laraba.

Ba a san ko wa ke da alhakin kai harin ba da aka kai shi mako guda bayan ‘yan IS sun kashe wani malami da ke goyon bayan ‘yan Taliban a wani harin kunar bakin wake a Kabul.

Tuni jami’an tsaro suka rufe wajen da lamarin ya afku.

Ganau sun bayyana yadda suka ji karar fashewar wani abu da har ya shafi tagogin wasu gidaje da ke kusa da masallacin.

Wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa yana kalllon yadda mutane ke fita ta taga da kuma gawarwakin mutane da dama.

Leave a Reply