Labarai

Rundunar ‘Yan sanda A Bauchi Na Bincike Kan Yaron Da Aka Kwakule Masa Ido

Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya ta tabbatar da tsintar wani yaro da aka kwakule wa idanu, a anguwar Dutsen Jira da ke nan Bauchi.

Wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Juma’a ta ce da misalin karfe shida na yamman ranar Alhamis ne aka ankarar da jami’na tsaron cewa na tsinci Uzairu Salisu, mai shekaru 16, kwance cikin jini wasu da kawo yanzu ba a san ko su waye ba, suka kwakule mashi ido.

A cewar matashin wani mutum da ya kira Ibrahim Rafin Zurfi ne ya neme shi da ya zo ya mishi aiki a gonar shi, to amma bayan sun isa sai ya shake shi da waya, ya kuma kwakwale masa ido.

Yanzu haka rundunar ta ce matashin na jinya a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa da ke Bauchi.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Bauchi CP Umar Mamman Sanda ya ce suna gudanar da bincike kan batun.

Ya sha alwashin kamawa da hukunta mutanen da suka yi wannan mummunar aika-aika.

Leave a Reply