Jamaâa a Æaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun ce sun shiga tsaka mai wuya sakamakon yadda ‘yan bindiga suka mamaye garuruwansu, kuma suka mayar da su tamkar bayi.
Mazauna yankin sun ce Æ´an bindigar sun kwace gonakin jama’a, tare da tilasta wa mutanen garuruwan yi masu shuka da huÉa da ma sauran ayyukan gona.
Yanzu haka dai jamaâar da Æ´an bindigar suka mamaye a yankin Æaramar hukumar Faskarin ta Najeriya suna cikin Æunci da damuwa.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa BBC cewa Æ´an bindigar suna shiga Æauyuka kuma su yi abin da suke so, kuma a lokacin da suke so.
Ya ce ââA yanzu maganar da ake a cikin firamare din Kogo Æ´an bindiga ne a ciki zaune, in an yi abinci a kai masu, in suka ga yarinya su Éauka, in kuma ka yi magana su kashe ka.ââ
Mutumin ya ce mazauna yankin suna biyayya ne ga Æ´an bindigar saboda basu da wani zaÉi na daban.
ââtashin farko dai suka sa aka haÉa masu kuÉi cikin yarjejeniyar da aka yi, da kuma gonakin da suka ware waÉanna ba za a noma ba, su za a nomawa. Duk lokacin noma za mu je can, mu yi masu hu mu yi masu noma, mu yi masu huÉa, su faÉa mana abin da za a noma, mu yi noma kuma idan lokacin girbi ya yi mu kwashe mu basu. Sun maida mu tamkar bayi a cikin wannan yanki, idan ka yi kaifi a hukunta kaââ.
Ya ce Æauyukna yankin da suka haÉa da Birnin Kogo da Yar-tsamiya da Kahi da Fankama da Hayin Dungu da kuma Gobirawa duk ÆarÆashin ikon Æ´an bindigar suke, waÉanda ke ci gaba da murgunawa jamaâa.
Dr Nasir Muâazu, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina ya ce gwamnatin jihar ta farga da wannan lamari.
ââMutane a irin waÉannan Æauyuka sun je sansanin Æ´an gudun hijira, to kuma wasu da yawa ba za su iya haÆuri da zaman sansanin ba don haka sai suka koma Æauyukan su, suna ci gaba da zama bisa ga yadda Æ´an bindigar suke ta gallaza masuââ
Dr Nasir ya ce gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda yana aiki tuÆuru don kula da mutanen da matsalar tsaron ta tilasta masu yin hijira da kuma tabbatar da tsaro a faÉin jihar.
Gwamnatin jihar Katsina dai ta lashi takobin magance matsalar tsaro da ta dabaibaye garuruwa da Æauyuka da dama na jihar. Kuma ko a kwanan nan sai da ta Æaddamar da rundunar sintiri ta farar hula don taimakawa wajen tabbatar da tsaro.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









