Skip to content
September 17, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Yan Sanda Sun Kama Wani Kan Zargin Yunkurin Kisan Kai da Satar Babur a Bauchi

July 25, 2025 3 minutes read

By Muhammad Sani Muazu

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wani mutum mai shekaru 40, Jibrin Iliya, bisa zargin yunkurin kisan kai da satar babur a unguwar Sabon Layi da ke cikin garin Bauchi.

A cewar sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na ‘Yan Sandan Jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, lamarin ya faru ne a ranar 20 ga watan na shekarar Yuli, 2025, da misalin karfe 6:00 na yamma, lokacin da rundunar ta samu rahoton cewa wasu matasa a Sabon Layi sun cafke wasu mutum biyu da ake zargin sun yi yunkurin hallaka wani dan Achaba.

Jami’an ‘yan sanda sun garzaya wurin, inda suka kama Iliya, yayin da abokin aika aikansa ya tsere.

Binciken farko farko ya nuna cewa wanda ake zargin tare da abokinsa sun haɗa baki ne suka hau babur ɗin Sa’adu Manniru, mai shekaru 30, mazaunin Kofar Wambai, a cikin garin Bauchi, da nufin sace babur ɗin.

Da suka isa wani wurin da suka tsara, sai suka kai masa sara da adda, suka buga masa a kai lokacin da ya tsaya domin karɓar kuɗinsa.

Ihun da ya yi ne ya ja hankalin mutane, inda suka bi bayan masu laifin har zuwa lokacin da ‘yan sanda suka iso.

Ana zargin sun yi ƙoƙarin guduwa da babur ɗin Bajaj ɗin Manniru mai lamba KTG 129 UV kafin aka kama su.

Lokacin da ake tuhumar Iliya, ya amsa cewa ya dade yana harkar satar babura na tsawon shekaru uku tare da wani abokinsa mai suna Lauwali daga karamar hukumar Numan ta jihar Adamawa.

Ya kuma amsa cewa sun saci babura uku a wurare daban-daban a Bauchi da Gombe, inda suka sayar wa wani mai saye a Gombe.

Iliya ya bayyana cewa ya karɓi Naira dubu talatin da Naira dubu ashirin a lokuta daban-daban daga cinikin baburan.

Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda ya ce za a ci gaba da bincike, kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu domin ya girbe abin da ya shuka.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya tabbatar da kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a fadin jihar, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da hadin kai ta hanyar samar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimaka wa aikin ‘yan sanda.

Karshen rahoton kenan, Zainab Umar Kudu, Duniya Zaman ‘Yan Marina

Tags: Bauchi State Government Bauchi state police command

Post navigation

Previous: Police Arrest Suspect for Attempted Murder, Motorcycle Theft in Bauchi
Next: National Population Commission Urges Gamawa Residents to Embrace Birth Registration

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.