Home Labarai Uwargidar Gwamnan Jihar Bauchi Ta Kai Ziyartar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Alhaji...

Uwargidar Gwamnan Jihar Bauchi Ta Kai Ziyartar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah, Ta Yi Addu’a Da Kuma Karfafa Gwiwar Iyalansa

Daga Zainab Faruk

Uwargidar Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Aishatu Bala Abdulkadir Muhammad, ta kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah, tsohon Hadimin Gwamna na Musamman kan Wayar da Kan Jama’a kuma Babban Mai Gabatar da Shirye-shiryen Gwamnatin Jihar Bauchi, wanda ya rasu kwanan nan.

A yayin jawabin nata ga iyalan mamacin, Hajiya Aishatu ta mika ta’aziyya gare su, musamman ga mata da ‘ya’yan mamacin da sauran dangi da abokan arziki. Ta bayyana mutuwar a matsayin jarabawa daga Allah da kuma tunatarwa ga kowa da kowa game da cewa duniya ba wajen zama ba ne.

“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Muna godewa Allah a kan kowanne hali da muka tsinci kanmu a ciki, domin mu bayi ne, kuma Allah yana gwada bayinsa da cuta, talauci ko mutuwa,” in ji ta.

Ta bukaci ‘ya’yan mamacin da su dage sannan su kyautata halayensu, su kasance masu neman ilimi da yin addu’o’i, inda ta bayyana cewa daya daga cikin mafi kyawun abin da uba zai bari a duniya shi ne ‘ya’ya nagari da ke yawan yi masa addu’a. “Hakkin mahaifinku yanzu ya dawo kan ku da mahaifiyarku. Ya wajaba ku kasance masu hankali, masu addu’a da kuma neman ilimi,” ta shawarce su.

Da take tuna halayen kirkin mamacin, Hajiya Aishatu ta yaba da yadda marigayin ke kasancewa cikin natsuwa da murmushi a koda yaushe, ba tare da nuna bacin rai ba. Ta ce: “Mutum ne da a ko yaushe idan ka ganshi yana cikin fara’a, ba a taba ganinsa cikin bacin rai. Wannan shi ne irin kyakkyawar gadon da ya bari.”

Ta kuma bukaci ‘yan uwansa da su ci gaba da hada kai da zama tare da juna cikin jituwa, musamman maza daga cikin ‘ya’yan mamacin da yanzu ke da nauyin kula da iyali. Sai dai ta jaddada cewa hakan ba ya nufin mata ba su da rawar takawa wajen neman ilimi ko sana’a. “Allah bai ce mata kada su nemi ilimi ko sana’a ba. Amma dai maza ne aka dora da alhakin kulawa da su.”

A karshe, ta juyo ga uwargidan mamacin, inda ta bayyana cewa nauyin da ke kanta yanzu ya ninka, kuma ta roki Allah ya ba ta ikon kula da ‘ya’yanta cikin tarbiyya da tsoron Allah. “Allah ya bude maki kofa daga cikin taskokinsa, ya ba ki ikon tarbiyyar ‘ya’yanki yadda ya dace,” in ji ta.

Hajiya Aishatu ta kammala ziyarar da addu’o’i na musamman ga marigayi Alhaji Jafaru Ilelah, inda ta roki Allah ya gafarta masa, ya karbi ibadunsa ya masa rahama, ya azurta iyalansa da zumunci da karfin guiwa da kuma zaman lafiya.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.