Ana fargabar cewa wasu âyan bindiga sun kwashe wani adadi da jamaâar kauyen Yola da ke Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin na zuwa ne bayan wasu âyan bindiga da ake zargin âyan daban daji sun kai hare-hare a yankuna daban-daban na kauyen.
Bayanai sun ce hare-haren da aka kai yankuna daban-daban sun yi sanadiyyar mutuwar jamaâa da dama yayin da aka yi garkuwa da wasu.
A cewar wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa, hare-haren sun auku a yankuna daban-daban na kauyen da ba zai iya fayyace adadin mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ba.
âNa samu labarin cewa a rana ta farko sun sace mutum huud sannan sun kashe wasu mutum biyu.
âHaka kuma a rana ta biyu sun kashe karin wasu mutum biyu tare da garkuwa da mutum daya.
âSai dai ba ni da tabbaci kan alkaluman mutanen da aka sace ko aka kashe.
âAmma ba na tantamar cewa an dauke wasu mutane kuma an kashe wasu.
âAbin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne Karaye tana bukatar dakarun soji su kawo mana dauki saboda wadannan hare-hare,â a cewarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa, a bayan nan yankunan Karamar Hukumar Karaye da Rogo na fuskantar matsalolin tsaro saboda kusancinsu da Jihohin Kaduna da Katsina.
Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne wasu âyan daban daji suka kashe wani mutum daya tare yin garkuwa da wani dan kasuwa a Kauyen Gangarbi da ke Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Nasiru Naâayya.
Kazalika, a shekarar 2021 ce Masarautar Karaye ta yi koken yadda ake samun kwararowar masu hakar maâadanai daga Jihar Zamfara.
Wasu majiyoyi sun ce tuni masarautar ta dauki matakam da suka dace domin yi wa tufkar hanci.
Sai dai ÆoÆarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin mai magana da yawun da rundunar âyan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura a yayin da bai amsa kiran wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









