Yan bindiga 21 sun sheka lahira bayan jamaâar gari da âyan banga sun yi musu kwanton Éauna a yankin Danko Wasagu na Jiajr Kebbi.
Shugaban Æaramar Hukumar Danko Wasagu, Hussaini Aliyu-Bena, ya ce âyan bindigar na tsallakowa zuwa Jihar Kebbi daga yankin Mariga na Jihar Neja ne, âyan banga da jamiâan tsaro suka yi musu kwanton Éauna a Tudun Bichi suka kashe 21 daga cikinsu.
Ya bayyana cewa Æaramar hukumarsa ta yi iyaka da yankin Mariga, shi ya sa âyan taâaddan suke samun sauÆin tsallakowa zuwa Jihar Kebbi ta nan.
Ya ce âyan bindiga sun kashe Marafan Mai Inuwa da ke yankin Kanya, suka yi garkuwa da wasu mutane, amma daga baya sojoji sun Æwato mutanen.
Ya roÆi gwamnati ta girke Æarin sojoji a yankunan Malekachi da Dankade, inda âyan bindiga suke bi su wuce.
Sannan ya yaba da ÆoÆarin jamiâan tsaro da âyan banga da sauran mazauna yankin wajen daÆile ayyukan âyan bindiga.
Shugaban Karamar Hukumar ya ce Gwamna Nasiru Idris ya ba da umarni a ziyarci alâummar Æauyukan da suka yi gudun hijira zuwa yankin Kanya a jajanta musu.
Aminiya ta nemi samun Æarin bayani daga kakakin âyan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, amma ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu rahoto ba tukuna.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









