Home Labarai Amarya Da Ango Zasu Angwance A Gidan Kaso

Amarya Da Ango Zasu Angwance A Gidan Kaso

Wata kotun shari’ar musulimci mai lamba 2 da ke Tashar Babiye a karamar hukumar Bauchi , ta aike da amarya da ango zuwa gidan gyaran hali, su ci amarcinsu a can, kafin ranar da za a yanke musu hukunci, bayan kotun ta samunsu da laifin hadin baki, da muzguna wa dan kishiyarta, tare da jimasa munanan raunuka.

Tin da farko ‘dan sanda mai gabatar da ‘kara Luka Godiya, yace a ranar 19 ga watan Agusta na wannan shekarar ta 2022, da misalin karfe 12 na rana, wasu membobin ‘yan kwamitin unguwar Bauchi, da ke cikin garin Bauchi, suka garzaya ofishin yan sanda suka kai karar wani mai suna Yusuf sani, da amaryarsa Na’ima Ahmed, wanda aka samesu da hada baki, da muzguna wa dansa, da yi masa azaba, kana da masa horo da kin bashi abinci, da mummunar duka ga yaron mai suna Walid Yusuf dan shekara 6, wanda saboda dukan Walid ɗin yasa ya samu munanan raunuka a jikinsa, da idonsa.

Dan sandan ya kara da cewa a lokacin da yaga Walid ɗin bai taba tunanin zai rayuba, sakamakon irin halin da ya ganshi ciki.

Luka Godiya, ya kuma ce, ana dukan yaron ne, saboda da babu mahaifiyarsa a gidan, kana mahaifin yaron ma yana dukan yaron, da kuma kishiyar mamansa, wato amaryan babansa kenan.

Amaryar takan daure yaron a gida, wani lokaci ma takan aiki yaron gurin da bai dace ace dan shekara 6 yana zuwa gurin, ko ana aikansa da daddare ba.

Aikata hakan laifine da yasaba wa kundin laifuffuka sashi na 125,213, 217, na tsarin dokar Penel Code.

Bayan karantawa amarya da ango kunshin tuhumen tuhumen da ake musu, sun amsa laifinsu.

Inda Mai shari’a Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya aike da mahaifin yaron tare kishiyar mahaifiyarsa, zuwa gidan gyaran Hali, ya kuma daga sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Agusta na shekarar 2022.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.