An ja kunnen al’ummar jihar Bauchi da su dauki matakan da suka dace domin dakile illolin ambaliya musamman ta hanyar share magudanun ruwa da aka bayyana a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasawa.
Hakan dai ya biyo bayan wata tattaunawa ce tsakanin Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Bauchi (BASEPA) da Hukumar Wayar da Kan al’umma (NOA) wajen neman hanyoyin magance matsalar.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar hasashen yanayi ta kasa NiMET ta yi hasashen cewa jihohi goma sha tara a Najeriya ciki har da Bauchi za su fuskanci mamakon ruwan sama a watan Satumban 2022 wanda zai iya haifar da ambaliya.
A nasa jawabin, babban daraktan hukumar kare muhalli ta jihar Bauchi (BASEPA) Dr. Ibrahim Kabir ya ce hukumar ta dauki isassun matakan da ya dace, sai ya bukaci mazauna jihar Bauchi da su kara kaimi domin samun sakamako mai kyau.
Ya kara da cewa hukumar ta bullo da wani shiri mai taken, “gidana, magudanar ruwa na” inda kowace unguwa ke da alhakin tattara sharar magudanar ruwa a yankinsu zuwa wurin da jami’anta za su kwashe.
A cewarsa, kin yin hakan zai sa a umarci kowace unguwa da su tsaftace muhallinsu tare da kwashewa da kansu.
Tun da farko mataimakiyar daraktan hukumar wayar da kan al’umma ta kasa Misis Theresa Magaji wacce ta wakilci Daraktan Alhaji Nuru Yusuf Kobi ta ce illar ambaliyar ruwa kamar asarar rayuka da dukiyoyi da kuma yaduwar cututtuka ya sa hukumar taga dacewar ta wayar da kan al’umma.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.