Latest:
Labarai

An dakatar da duk wani Ma’aikacin Gwamnatin da aka dauka daga ranar 1 ga Octoban 2022 – Gwaman jihar Pilato

 

Gwamnan jihar Pilato, Caleb Mutfwang ya bayar da umurni dakatar da ma’aikatan gwamnatin da aka dauka a jihar daga ranar 1 ga watan Octoban shekara ta 2022, yana mai fadin cewar an bayar da aikn ba bisani ka’ida ba.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan watsa labarai da Hulda da jama’a na Gwamnan, Gyang Bere.

Sanarwar ta kuma umurci dukkanin ma’aikata da wadanda aka nada amatsayin manyan sakatarorin gwamnati daga watan Junairun 2023 da su koma amatsayin da suke Kai kafin musu wannan karin girman .

Sanarwa ta kuma kara da cewar, an kuma dakatar da duk wani ma’aikacin da aka dauka daga watan October, 2022, tare da sake duba tsarin da aka bi aka daukesu aiki.

Sanarwar tace an dauki wadannan matakan ne domin farfadowa da inganta aikin gwamnatin jihar tare da bin tsari yadda yakamata

Leave a Reply