Home Labarai An Garzaya Da Aung San Suu Kyi Gidan Yari

An Garzaya Da Aung San Suu Kyi Gidan Yari

Gwamnatin soji a Myanmar ta kai tsohuwar Shugaba Aung San Suu Kyi gidan yari mai tsananin tsaro da ke birnin Nay Pyi Taw.

Dama Aung San Suu Kyi na fuskantar daurin talala ne a wani boyayyen wuri, bayan da kotu ta yanke mata shekaru 11 bisa kamata da laifin cin hanci da rashawa.

Sojoji sun kifar da gwamnatin tsohuwar Shugabar mai shekaru 77 a watan Fabrairun 2021.

Sai dai kafin nan ta rasa martabarta a idon duniya, bayan da ta goyi bayan muzgunawar da sojojin ke yi wa musulmin kabilar Rohingya.

Hakan yasa ta rasa lambar girmamawa ta ‘Nobel Laureate Prize’ kan zaman lafiya.

Yanzu haka Aung San Suu Kyi na fuskantar karin wasu zarge-zargen, da zasu sa a iya yanke mata daurin sama da shekaru 190 a gidan yari.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.