Labarai

An Kama Yan Najeriya A London

Yan sanda a Birtaniya sun kama mutane biyu daga Najeriya da zargin shiga kasar da karamin yaro da nufin cire wani sashe na jikinsa.

‘Yan sandan sun bayyana sunayensu a matsayin Ike Ekweremadu da Beatrice, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu yau Alhamis.

Kazalika ‘yan sandan sun ce yanzu haka yaron na hannun hukumomin da ke kula da kananan yara.

Sun ce an kaddamar da bincike ne bayan jami’an tsaro sun ankara kan batun, a karkashin dokar bauta da aka samar a kasar watan da ya gabata.

Leave a Reply