Labarai

Dan Majalisar Jihar Anambra Ya Yi Mutuwar Farat Daya A Afirka Ta Kudu

Wani dan majalisar Jihar Anambra ya mutu yayin wata ziyara da ya kai kasar Afirka ta Kudu.

Marigayin mai suna Nnamdi Okafor shi ne shugaban masu rinjaye a majalisar, kuma shi ke wakiltar mazabar Awka ta Kudu ta 1 a majalisar.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa dan majalisar ya yi mutuwar farad-daya ne a wani otel da ke Sandton City na birnin Johannesburg da safiyar Laraba, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa bayan da aka garzaya da shi asibiti.

Ba a san abin da ya janyo mutuwar tasa ba.

Wasu ‘yan majalisar Jihar ta Anambra sun tafi Afirka ta Kudu domin su halarci wani kwas da majalisar ta shirya.

Gwamnan Jihar Charles Soludo ya tabbatar wa manema labarai mutuwar Mista Okafor.

Leave a Reply