Home Labarai An kori Shugaban Tsangayar horas da Aikin Shari’a na Jami’ar Kalaba bisa...

An kori Shugaban Tsangayar horas da Aikin Shari’a na Jami’ar Kalaba bisa zargin Lalata Da Ɗalibai

 

Jami’ar Kalaba ta cire Shugaban Tsangayar Aikin Lauya, Farfesa Cyril Ndifon daga matsayinsa tare da dakatar da shi daga aiki, saboda zargin da ɗalibai mata ke masa na yin lalata da su.

Shugabar Jami’ar Farfesa Florence Obi ta kuma haramta wa lakcaran, wanda ya yi ƙaurin suna kan lalata da ɗalibai masu kananan shekaru, daga shiga harabar jami’ar, sai idan kwamitin binciken zargin da ake masa ne ya neme shi.

Kwamandan Boko Haram Da Ya kashe Mayaƙa 82 Ya Miƙa Wuya

Karo na biyu ke nan daga shekarar 2015 da zargin lalata da ɗalibai ya sa jami’ar ta dakatar da Cyril Ndifon, wanda shi ne ɗan asalin Jihar Kuros Riba na farko da ya zama farfesa a fannin aikin lauya.

Sanarwar da Rajistaran jami’ar ya fitar ta ce an dakatar da Farfesa Cyril ne saboda zargin sa da saɓa dokokin jami’ar.

Dakatarwar ta fara aiki ne daga ranar 18 ga Agusta 2023, bayan rashin gamsuwar Shugabar Jami’ar da bayanin Farfesa Cyril Ndifon game da zargin da ɗaliban nasa mata ke masa.

A ’yan kwanakin da suka wuce ne ɗalibai mata daga Tsangayar Aikin Lauya ta jami’ar ɗauke da kwalaye suka yi zanga-zangar neman a sallami Farfesa Ndifon bisa zargin sa da lalata da su.

Jaridar Aminiya


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.