Kwamandan Boko Haram da ya yi sanadin kashe mayaÆan kungiyar 82 a rikicin Æabilanci da ya Éarke a tsakaninsu ya miÆa wuya ga sojoji.
Amir din Tsibirin Bukkwaram ya miÆa wuya ga sojojin Najeriya da ke Rundunar HaÉin Gwiwar Æasashe (MNJTF) ne tare da iyalansa da wasu mayaÆa, inda suka sallama makamansu da dabbobi.
âDon kashin kanya ya mika wuya tare da iyalansa da wasu mayaka kuma sun sallama makamansu da dabbobi,â in ji wata majiyar soji, wadda ta ce suna hannun dakarun rundunar Operation HaÉin Kai na MNJRF da ke Monguno, Jihar Borno.
Ta ci gaba da cewa, âCafke Amir Éin Bukkwaram gagarumar nasara ce saboda yana cikin manyan miyagun kwamandojin Boko Haram masu fikira kuma yana cikin masu Éaukar mayaÆa a yankin Tafkin Chadi.â
Aminiya ta kawo rahoton yadda rikicin Æabilanci na cikin gida a Æungiyar Boko ya sa mayakanta 82 kashe juna a Jihar Borno.
Rikicin ya Éarke ne bayan Amir Bukkwaram ya sa an harbe wasu mayaÆansa bakwai âyan Æabilar Buduma bayan yunÆurinsu na miÆa wuya ga sojoji bai yi nasara ba.
Matakin ya haddasa Æazamin faÉan Æabilanci tsakanin mayaÆa âyan kabilun Buduma, Fulani, Kanuri da Hausawa a inda 82 daga cikinsu suka mutu.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








