Latest:
Labarai

Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Kori Wasu Ma’aikata Biyu Daga Bakin Aiki Bisa Badakala Da Kudin Fansho

 

Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta jihar Bauchi ta kori wani mutum maisuna Nasiru Sama’ila da kuma Auwal Jibrin dukkansu dasuke a ma’aikatar kudi bisa samunsu da laifin saɓa ka’idar aiki.

An yanke wannan shawarar ne yayin zama na 18 da Hukumar tayi ranar 15 ga Agusta, 2023 a dakin taro na Hukumar.

Cikin wata sanarwar dauke da sa hannun Saleh Umar ya ce yayin zaman tattaunawar kan ladabtar da jami’an biyu an same su da laifin yin jebun takardun da suka ba su damar karkatar da kudaden da suka kai dubu dari uku da talatin da biyu mallakin wani tsohon ma’aikaci da ya rasu mai suna Jibrin Adamu Zalanga.

Ma’aikatan da ake zargin sun amsa laifin da ake zarginsu da aikatawa a cikin martanin tambayoyin da ma’aikatar ta yi musu.

A cewar sanarwar, dokar ta sabawa sashe na 327 na dokokin aikin gwamnati.

A hannu guda kuma, Hukumar ta kuma yi karin girma ga jami’ai 73 tare da amincewa da sauya wa jami’ai 11 wajen aiki inda ma’aikatar kula da harkokin addini ta dauki nauyin daukar ma’aikata 59 zuwa mataki daban-daban.

Shugaban Hukumar Alhaji Abubakar Usman wanda ya jagoranci zaman tattaunawar ya ce al’amuran da suka shafi ladabtar da kudi sun zama masu daure kai ga hukumar don haka ya bukaci ma’aikatan jihar da su yi aiki bisa ka’idojin hukumar wajen sauke dauyin dake kansu.

Idan za a iya tunawa dai a kwanakin baya ne Hukumar ta dakatar da wani Ibrahim Garba da ke aiki a hukumar fansho ta jiha irin wadannan laifukan.

Leave a Reply