Hukumar kula da ayyukan gwamnati ta jihar Bauchi (CSC) ta kori wani mai suna Ibrahim Garba, babban mataimakin sakatare da ke aiki a hukumar fansho ta jihar daga aiki.
Hukumar ta amince da dakatarwar ne a zamanta na 17 da ta gudanar a ranar 1 ga watan Agustan 2023 a dakin taron na hukumar.
An samu jami’in ne da laifin aikata saba ka’idojin aiki da cin amana saboda shigar da kansa cikin badakalar albashi/fensho kuma matakin da ya dauka ya saba wa ka’idojin ma’aikatan gwamnati da suka shafi almubazzaranci da kudade.
Ibrahim Garba wanda kwamitin ladabtarwa na hukumar fansho ta jihar ta same shi da laifin yin wayo da canza asusun ajiyar wani mai suna Audu Mohammed, wanda yanzu ya rasu, da lambar asusunsa wanda ya sauwake wurin biyan albashi bayan dan uwan mamacin ya bayar da rahoton rasuwarsa.
Daga nan Ibrahim Garba ya karbi fansho na watanni hamsin da biyar (55) ba bisa ka’ida ba wanda kudin yakai N54,871.26 Akowace wata na tsawon shekara hudu na watanni bakwai wanda ya kai sama da naira miliyan uku.
Shugaban Hukumar Alh. Abubakar Usman wanda ya jagoranci zaman yayi kira ga ma’aikata a jihar dasuji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu.
Yace dole ne a kiyaye ka’idojin aikin gwamnati tare da kiyaye su ya kuma tabbatar da cewar za,ayi amfani dashi a inda ya dace don tsaftace tsarin ta yadda za a gudanar da hidimar a bayyane.
Shugaban hukumar ya tabbatar wa da ma’aikatan gwamnati cewa babu wani ma’aikaci da za a ci zarafinsa kuma hukumar bazata nade hannunta tana gani wasu bata gari suna kokarin lalata aikin gwamnati duk da kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta magance dukkanin matsaloli awani mataki na kawo cigaban jihar.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.