Labarai

Wani Magidanci ya yi garkuwa da matarsa tsawon shekara 12

 

Yan sanda sun cafke wani magidanci kan zargin ya yi garkuwa da matarsa na tsawon shekaru 12 a cikin gidansu.

Mutumin mai shekaru 55 dan kasar Jamus ya shiga hannu ne bayan an gano matar tasa kusan a tsirara, da kanta a aske a cikin mawuyacin hali a gidansu da ke kasar Faransa, a kan iyaka da kasar Jamus.

Matar ta mai shekaru 53 ta shaida wa jami’an tsaro cewa mijin nata ya yi garkuwa da ita na tsawo shekara 12, amma ya musanta, inda ya ce tana fama ne da cutar kansa, kuma yana kula da ita.

’Yan sanda sun ce an gano matar ne bayan da ta sanar da jami’an tsaron kasar Jamus ta wayar tarho, inda su kuma suka sanar da takwarorinsu na Faransa, suka kai samame gidan.

Wasu rahotanni sun ce gano matar, wadda ita ma ’yar kasar Jamus ce a uwardakan gidan nasu a kanjame, yunwa ta tagayyara ta, kanta a aske, ga raunuka a jikinta, wanda ake zargin an azabtar da ita.

Jami’an lafiya sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa matar, ba ta da koshin lafiya.

Wani jami’in hukumar ya ce gwajin aka yi wa matar ya nuna babu ruwa sosai a jikinta, sannan akwai tufka da warwara a bayanan da ta yi wa masu bincike.

Wamma ya ce sakamakon gwajin da aka gudanar ya nuna babu tabbai ko karaya a jikin matar yadda kafofin yada labaran Faransa suka yayata.

– Baki biyu

Ya bayyana cewa da alama “matar ta fara sauya baki daga zargin azabtarwa, ta koma batun rashin gamsuwa da halin da take ciki da kuma irin kulawar da take samu a matsayin mara lafiya.”

Ya ce sankonta na da alama da cutar kansa, sannan an same ta dangalallun kayan jikinta ne saboda da sassafe aka kai samamen kama mijinta.

– ‘Shekara 10 da suka wuce’ –

Wata makwabciyar ma’auratan ta ce kimanin shekara 10 da suka wuce mutumin ya sanar da dukkansu cewa matarsa na fama da ciwon kansa.

“Ban taba ganin ta ba, ina ganin ba taba fita daga gida ba,” in ji Alicia, wadda ta ce “Wani lokaci nakan ji ta yi kara,” wanda take zargin zafin ciwon ke sa matar yin hakan.

Amma ta ce mutumin “yana da mutunci da kirki”.

Wata makwaciyarsu mai suna Erika, ta ce rabonta da ganin matar “ya kai shekara 10”, don haka ta yi zaton “ta rasu ko kuma ta bar gidan”.

’Yan sanda na gudanar da bincike domin gano gaskiyar zargin da matar ke wa mijin nata na azabtarwa, kamar yadda kafar yada labaran Faransa, BFMTV ta ruwaito.

Wasu rahotanni sun ce an gano wani kundi a gidan wanda a cikin magidancin ya rubuta bayanan lokutan da ya ba ta abinci da magani; ko da yake hukumomi ba su tabbatar da rahoton ba.

’Yan sanda sun ce an taba kiran su zuwa gidan ma’auratan a shekarar 2019, amma ba su ga alamar wata matsala ba a lokacin.

Yanzu dai ana tsare da mutumin domin ci gaba bincike.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply