Home Labarai Bai kamata a ce Nijeriya na fama da talauci ba, cewar Tinubu

Bai kamata a ce Nijeriya na fama da talauci ba, cewar Tinubu

 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a jiya Alhamis ya ce bai kamata a ce Nijeriya na fama da talauci ba, kasancewar ƙasar na da dimbin albarkatu na al’umma da ma’adanai.

A wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mashawarci na musamman kan harkokin yada labarai ga shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya fitar a Abuja, Tinubu ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa a karkashin shugabancinsa za a yi amfani da albarkatun yadda ya kamata domin amfanin ƴan kasa.

Ngelale ya ce shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wata ganawa da tawaga mai wakilai 62 daga Jihar Rivers, da suka hada da shugabannin jam’iyyar APC, da kuma jam’iyyar adawa ta PDP, a fadar gwamnati, Abuja.

“Bai kamata mu kasance a talauci ba. Dole ne mu tashi tsaye! ko ta yaya a cikin wannan guguwar, akwai wurin aminci da kwanciyar hankali a gare mu. Za mu gano shi!

“Mu ba malalata ba ne, muna da wadata da yawa. Muna bukatar mu zama muna taimakawa junan mu, kuma maƙwabta nagari ga juna. Ni ba Shugaban kasa ba ne da zai ba da uzuri.

“Zan yi aiki tukuru ga al’ummarmu da manufa, jajircewa da sadaukarwa, don samar da arziki ga daukacin ƴan Najeriya., ba mu da dalilin zama matalauta! Ba za mu waiwaya baya ba, za mu yi gaba ne kawai don neman mafita,” in ji Tinubu.

Daily Nigerian Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.