Home Labarai Bansan Me Nayi Aka Kama Ni Ba – Muhuyi Magaji

Bansan Me Nayi Aka Kama Ni Ba – Muhuyi Magaji

Tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya tabbatar wa BBC Hausa kama shi da ‘yan sanda suka yi amma ya ce ba a faɗa masa laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

‘Yan sanda sun kama tshohon shugaban ne wanda ke neman tsayawa takarar gwamnan Kano a babban zaɓe na 2023 a Abuja yayin da ya je aikin tantancewa da jam’iyyar PDP ta shirya.

“Babu wanda ya faɗa min dalilin da ya sa aka kama ni, ba a faɗi wani laifi ba a takardar izinin kama ni,” in ji Muhuyi cikin wani saƙo da ya aike wa BBC.

Wata takarda da aka gabatar wa Muhuyi ta nuna yadda wata kotun majistare a Kano ta ba da umarnin kama shi.

Ya

Yanzu haka yana tsare a ofishin ‘yan sanda na Abuja, babban birnin Najeriya.

Gwamnatin Kano ƙarƙshin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dakatar da Muhuyi ne daga muƙaminsa bayan zargin sa da badaƙala a wasu kwangiloli da kuma aringizo tare da ƙaddamar da bincike kan sa a watan Yulin 2021.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.