Breaking NewsLabarai

Jami’an Tsaro Sunyi Ram Da Muhuyi Rimingado A Abuja

Rahoton da muke samu na cewa jami’an ‘yan sanda sun kama tsohon shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin-hanci da rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Muhuyi Rimingado.

Jaridar Dailly Nigerian Hausa ta ce an kama Rimingado ne a masaukin Gwamnan Sokoto da ke  babban birnin tarayya Abuja, yayin da ya je domin a tantance shi a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP.

An jiyo cewa ƴan sandan sun tafi da Rimingado nan da nan bayan an tantance shi, inda su ka wuce da shi shelkwatar rundunar ‘yan sanda da ke Abuja.

Majiyoyi na tsaro sun ce za a wuce da shi Kano domin a gurfanar da shi a gaban kotu.

Idan za’a iya tunawa dai an dakatar da Rimingado ne a watan Yulin shekarar da ta gabata (2021) bayan buɗe bincike kan badaƙalar kuɗi da aringizon kuɗaɗen kwangiloli da a ke zargin an baiwa wasu kamfanoni masu alaka da dangin gwamna.

Leave a Reply