Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana jin daÉinsa kan hukuncin da kotun Æararrakin zaÉen shugaban Æasa ta yanke.
Wanda ya tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaÉen shugaban Æasar da aka gudanar a watan Fabrairu.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban Æasar, Mallam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce kotun Æararrakin zaÉen shugaban Æasar ta “kafa tarihi” ta hanyar yin watsi da duk wata barazana da zarge-zarge marasa tushe wajen yanke hukunci cikin gaskiya da adalci, don martaba zaÉin ‘yan Najeriya.
Buhari ya ce “duk wanda ya yi nasara a yau dimokraÉiyya da al’umma ne suka yi nasara, idan Kotun Æoli ta yanke hukunci, to an gama da batun zaÉe lokaci ne da ya kamata Æurar zaÉe ta kwanta”.
“Gwamnatin APC ÆarÆashin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ta samu goyon bayan kowa domin cika alÆawuran da ta Éaukar wa al’umma”, in ji Buhari.
Toshon shugaban Æasar ya kuma aike da saÆon taya murna ga shugaban Æasar Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da kuma jam’iyyar APC kan wanna nasara da suka samu a kotu.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








