Home Labarai Cecekuce ya barke a zauren Majalisa kan shekarun wani da ake tantancewa...

Cecekuce ya barke a zauren Majalisa kan shekarun wani da ake tantancewa a matsayin minista

 

Bayanan shekarun, Farfesa Joseph Turlumum, da na karatun sa ya janyo zazzafar muhawara a zauren majalisar dattajan Najeriya, a lokacin da ake tantancesa a matsayin minista.

Farfesa oseph Turlumum ya fito daga jihar Benue kuma ya na cikin jerin sunayen da shugaba Tinubu ya aika a zaunen majalisa domin tantancewa

Majalisar Dattijan Najeriya ta fara tantance mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya aika mata don neman amincewarta kafin ya naɗa su ministoci.

Na farko a cikin mutanen da aka tura sunayensu su 28, shi ne Abubakar Momoh daga jihar Edo.

A matsayinsa na tsohon ɗan majalisar wakilai, Abubakar Momoh bai fuskanci tsauraran tambayoyi kafin Shugaban Majalisar Ɗattijai Godswill Akpabio ya buƙaci ya risina wa majalisa, ya wuce.

Mutum na biyu da ya bayyana a zauren majalisar, shi ne Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas.

Babu masaniya kan adadin mutanen da majaisar za ta tantance a Litinin ɗin nan, ranar farko da fara wannan aiki.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai aika da ƙarin sunaye, kamar yadda tsarin mulkin ƙasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.