Wani dalibin Jamiâar Jihar Gombe da ke zangon karatu na karshe mai suna Abubakar Muhammad, ya rasu yayin da yake tsaka da rubuta jarrabawar kammala makarantar.
Dalibin dai na karatu ne a sashen koyon aikin Akanta na jamiâar.
Wani abokin karatun marigayin ya bayyanawa wakilinmu cewa marigayin ya zo dakin rubuta jarrabawa a ranar sai rashin lafiya ta kama shi inda nan take aka garzaya da shi zuwa cibiyar lafiya ta jamiâar dan duba lafiyarsa.
Sai dai a cewar majiyar, jikin dalibin ya tsananta, amma kafin nan rai ya yi halinsa, inda aka wuce da shi dakin adana gawarwaki a asibiti.
âYa rasu a cibiyar lafiya ta jamiâar sannan daga bisani mataimakin shugaban sashen tsaro na jamiâar ya jagoranci daukar gawar zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin kwararru na Jihar Gombe tare da wasu abokansa da kuma wasu jamiâan jamiâar,â in ji dalibin.
Da wakilinmu ya tuntubi jamiâin hulda da jamaâa na jamiâar, Mohammed Abubakar, ya tabbatar da rasuwar dalibin.
Sai dai ya ce dama dalibin ba shi da lafiya a ranar tun kafin shigarsa dakin zana jarrabawar.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









