Home Labarai Dalilin da yasa Tinubu ya yi wa Jakadun Najeriya kiranye

Dalilin da yasa Tinubu ya yi wa Jakadun Najeriya kiranye

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkanin jakadun Nijeriya da su dawo gida.

Ministan kula da harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, shi ne ya shaida hakan a ranar Asabar.

A wata sanarwar babban hadimin ministan kan yada labarai da hulda da jama’a, Alkasim Abdulkadir, ya tabbatar da cewa dukkanin Jakadun Nijeriya an kirayesu da su dawo.

Sanarwar ta ce, “Bisa tambayar da ake ta yi dangane da wasikar kiranye ga jakadan Nijeriya a Ingila, ministan harkokin wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar, ya warware zare da abawa da cewa dukkanin Jakadun Nijeriya ne ma aka umarta da su dawo gida bisa umarnin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bada.

“Dukkanin Jakadun Nijeriya da suke wakilci a wasu kasashe suna karkashin umarnin shugaban kasa ne, kuma shi ne ke da ikon dawo da dukkanin wani daga kowace kasa.”

A cewarsa, fayyace hakikanin batun ya zama musu dole ne lura da kiran da aka yi wa Jakadan Nijeriya a kasar Burtaniya, Sarafa Ishola da ya dawo.

A wasika mai dauke da kwanan wata 31 ga watan Agustan 2023 da ministan harkokin wajen ya aika wa Ishola, Tuggar na cewa, “Ina farin cikin sanar da kai matakin da shugaban kasa ya dauka na maka kiranye, hakan da ke nuni da zuwan karshen wakilcinka a matsayin babban jakadan Nijeriya a kasar Ingila.”

Kan wannan, an umarci jakadan da cewa cikin kwanaki shida ya hada bayanan barin aiki sannan ana tsammanin zai dawo Nijeriya kafin ko zuwa ranar 31 ga watan Oktoba, 2023.

“Ina amfani da wannan damar wajen nuna godiyar shugaban kasa a gareka bisa gudunmawarka da ka bayar a matsayin babban jadakan Nijeriya a Burtaniya.

“A daidai lokacin da muke tsumayar dawowarka Abuja, shugaban kasa na mika godiyarsa gareka bisa hidimta wa Nijeriya na zama babban jakadanta. Ina maka fatan samun rayuwa mai kyau a nan gaba,” wasikar ta shaida.

Jaridar Leadership


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.