Hukumar zaÉe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, ta yi watsi da batutuwan da wasu Æ´an takarar shugaban Æasa suke yi cewa sun bayar da sunayen waÉanda suka zaÉa mataimaka a matsayin na riÆo.
A yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise a Najeriya, Éaya daga cikin Kwamishinoni na INEC, Festus Okoye ya bayyana cewa babu batun Éan takarar mataimakin shugaban kasa na riÆo a kundin tsarin mulki.
Ya bayyana cewa tuni duka Æ´an takarar shugaban Æasa suka bayar da duka sunayen mataimakansu ga hukumar INEC, ba wai mataimaka na riÆo ba.
Wannan lamari dai ya jawo ce-ce-ku-ce matuÆa inda jama’a da dama ke ganin me zai sa wasu daga cikin Æ´an takara su aikata wannan kuskure.
Ko a kwanakin baya sai da Tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso ya shaida wa kafar BBC cewa ya bayar da sunan wani mutum a matsayin mataimakinsa na riÆo ba na dindindin ba.
Ya bayyana cewa nan gaba idan ya kammala tuntuÉa da sauran masu ruwa da tsaki za su tura wa hukumar INEC sunan mataimaki na dindindin wanda zai maye gurbin wanda suka saka a yanzu.
Kazalika, a kwanakin baya an yi ta raÉe-raÉin cewa shi ma dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da sunan Kabiru Ibrahim Masari, wani dan siyasa dan asalin Jihar Katsina, a matsayin mataimakinsa na riÆo.
Sai dai Tinubu ya fito ya bayyana cewa an zaÉi Kabiru Masari ne, amma zai iya sauka zuwa wa’adin da hukumar zaÉe ta bayar yana mai cewa hakan bai saÉa wa doka ba.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








