Home Labarai EFCC ta kama tsohuwar Ministar mata Pauline Tallen bisa zargin Almundahana

EFCC ta kama tsohuwar Ministar mata Pauline Tallen bisa zargin Almundahana

 

Tsohuwar Ministar mata da walwala a mulkin tsohon shugaban kasar Muhammadu Buhari, Pauline Tallen a yanzu haka ta shiga hannun jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa wato EFCC sakamakon zargin ta da ake yi da almundahana.

Rahotannin sirri sun bayyana cewa Tallen tana amsa tambayoyi a hannun Jami’an hukumar EFCC a shalkwatar hukumar dake Wuse a birnin Abuja.

Dukkuwa da yake babu isassun bayanai akan zargin tsohuwar ministar amma majiyar da take da alaƙa da tuhumar nata tace ana zargin ta ne da almundahanan kuɗi aƙalla Naira biliyan 2.

Acewar majiyan, kuɗin da ake tuhumar ta da bai gaza Naira biliyan 2 ba kuma wani bangare na kuɗin an karkatar dashi ne daga wani shiri a nahiyar Afirka mai suna African First Lady Peace Mission Project a turance.

Ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto dai anyi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren amma abun yaci tura.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.