Home Labarai Farashin dala na cigaba da faɗuwa a Najeriya

Farashin dala na cigaba da faɗuwa a Najeriya

Farashin dala na faɗuwa a kasuwannin canjin kuɗaɗe a Najeriya daga naira 940 zuwa naira 890 a safiyar Laraba kamar yadda bayanan da BBC ta samu daga kasuwannin canji a birnin Legas da ke kudancin ƙasar suka nuna.

Bayanan sun nuna cewa a safiyar jiya Talata, an sayar da dalar kan naira 940, da yamma kuma, ta fadi zuwa naira 927 a kasuwannin canjin a Legas.

Wannan na zuwa ne bayan ganawa da muƙaddashin gwamnan babban bankin kasar, Folashodun Shonubi, ya yi da shugaba Bola Tinubu a ranar Litinin a fadarsa da ke Abuja, kan yadda za a farfaɗo da darajar Naira.

A kasuwannin canji na Abuja kuma, a safiyar Laraba, dalar ta fadi zuwa naira 900, inda a safiyar Talata, aka sayar da ita kan naira 947, da dare kuma, ta sauka zuwa 910.

Haka ma Kano da ke arewacin ƙasar, bayanai daga kasuwannin canji na nuna cewa dalar ta faɗi daga naira 946 a safiyar jiya Talata zuwa naira 900 a safiyar yau Laraba.

A daren jiya dalar ta fara sauka a kasuwannin canji na Kano inda ta sauka zuwa naira 927.

Wannan lamari na nuna cewa darajar kuɗin naira ta fara farfadowa.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.