Ana zargin garin kwaki ya yi ajalin wata yarinya tare da galabaita ’yan uwanta biyar a Jihar Kano.
Firdausi Mahmud Abdullahi ta rasu ne bayan cin garin kwaki da ta yi bayan da ta shafe tsawon lokaci ba tare da ta sanya wani abu a cikinta ba,a unguwar Rimin Hamza a yankin Karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano.
Tsananin tsadar rayuwa da aka shiga a Najeriya sakamakon janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya wanda ya sa magidanta da dama ba su iya ciyar da iyalansu.
Malam Mahmud Abdullahi shi ne mahaifin Firdausi ya shaida wa Aminiya cewa shi ne da kansa ya sayo garin kwakin ya kawo gida aka kwaɗanta wa yaran inda daga bisani ɗaya daga cikinsu ta ce ga garinku nan.
“To dama dai kun san irin yadda rayuwar ta koma, ba a samu a ci abinci kamar yadda ya kamata. To yaran nan sun tara yunwa a jikinsu.
“Bayan na fita neman abinci tun safe ban dawo ba sai bayan Magariba na shigo gidan da garin rogo. Shi ma kudin wani mutum ne ya ba ni kyautar Naira 500 sai na je na sayo garin kwaki na Kai gida aka kwaɗanta musu.
“Bayan sun ci wannan garin kwakin ne sai dukkanin yaran suka fice daga hayyacinsu suka kuma ɓarke da amai da gudawa.”
Malam Mahmud ya kara da cewa, “Kasancewar dare ya yi ba za mu iya tafiya asibiti ba, sai muka kira wani ma’aikacin lafiya inda ya duba su ya yi musu allurai tare da yi musu ƙarin ruwa. Sai dai wajen misalin ƙarfe daya na dare ita Firdausi ta ce ga garinku nan.”
A cewarsa shi bai ci garin ba sakamakon garin ba shi da yawa.
“Kasancewar garin gwangwani biyu ne shi ne ya sa ni ban ci ba, duba da cewa yaran sun yini ba su ci komai na fi tausayin su, don haka na ce a ba su su ci, ni na hakura.”
Malama Sadiya ita ce mahaifiyar marigayiya Firsausi, ta ce sauran ’yan uwan Firdausi biyar waɗanda suka ci abincin tare da ita su ma sun galabaita.
“Dukkaninmu muka ci garin lamarin da ya zame mana amai da gudawa. Ita Firsausi kasancewar ta fi sauran ’yan uwanta galabaita shi ne abin ya zo da ajalinta,” in ji ta.
Malama Sadiya ta ƙara da cewa a yanzu haka sai ta yi sana’ar wanki sannan suke ɗan samun abin da za su ci ita da ’ya’yanta shida.
“Ina yin sana’ar wankau a gidajen unguwa. Wani lokacin a gidan wankin za a ba ni abinci na taho da shi gida da ɗan kuɗin da na samu sai mu ɗan sayi wani abin mu haɗa mu ci.
“Wani lokacin ma kuɗin wankin ba a biya a kan lokaci sai na yi ta bi kafin a biya ni. Wallahi sai mu yi sati ba mu ɗora tukunya ba.”
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.