Labarai

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin sasantawa da ƴan bindiga a Zamfara

Ministan tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar ya musanta zargin da gwamnan jihar Zamfara ya yi na cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin sasantawa da ƴan bindiga.

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin X na ma’aikatar tsaron Najeriya, ministan ya ce gwamnatin tarayya ba ta umurci wani ko wasu su tattauna da ƴan bindiga a madadinta ba.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnatin Tinubu na aiki domin ceto sauran daliban Jami’ar Tarayya da ke Gusau, waɗanda aka sace a ranar Juma’a.

A cewar Badaru a yanzu haka sojoji sun ceto dalibai 13 da kuma leburori uku daga cikin mutanen da ƴan bindiga ke garkuwa da su.

A ranar Litinin ne gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare ya fitar da wata sanarwa inda ya zargi Gwamnatin Tarayya da yin tattaunawar sirri da ƴan fashin daji a jihar Zamfara ba tare da sanin gwamnatin jihar ba.

Sai dai da yammacin Litinin, wata sanarwa daga ofishin ministan yaɗa labaru da wayar da kan al’umma na Najeriya ta musanta batun, tare da zargin gwamnan na jihar Zamfara da ƙoƙarin siyasantar da batun tsaro.

Sai dai duk da haka gwamnan, ta hannun mai taimaka masa kan yaɗa labaru da hulɗa da jama’a ya sake fitar da wata sanarwar a ranar Talata inda ya ce gwamnatin jihar tana da shaidu na irin tattaunawar da ta gudana tsakanin jami’an gwamnatin tarayya da ƴan fashin dajin.

Masana tsaro na kallon musayar kalaman tsakanin ɓangarorin biyu a matsayin wani abu da ka iya yin cikas ga ƙoƙarin gwamnati na yaƙi da ayyukan ƴan fashin dajin a yankin na arewa maso yammacin Najeriya.

BBC Hausa