Labarai

Ambaliyar Ruwa Ya Hallaka Mutum 16 A China

Ambaliyar ruwa da zaftarewar kasa a arewa maso yammacin China sun kashe mutu 16, yayin da wasu da dama kuma suka bace.

 

Kafar yada labaran kasar ta rawaito cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a lardin Qinghai a wannan makon, ya janyo koguna da tekunan yankin sun cika makil abin ya janyo garuruwa da kauyukan suka kasance ruwa ya mamaye su.

Tuni aka tura jami’an agajin gaggawa dubu biyu zuwa yankin.

China dai na fuskantar mamakon ruwan sama a wannan shekarar abin da ya janyo aka samu ambaliya a wasu wurare.

Leave a Reply