Labarai

‘Yan Bindiga Sunyi Awon Gaba Da DPO A Jihar Nasarawa

Rahotanni daga jihar Nasarawa da ke tsakiyar Najeriya na cewa an yi garkuwa da shugaban jami’an yan sanda na karamar hukumar Nasarawa-Eggon.

Rahotannin sun ce CSP Haruna AbdulMalik na sintiri ne a ranar Laraba da daddare tsakanin Eggon-Akwanga, a lokacin da yan bindiga suka fara harbi ba-ji-ba-gani, kafin su yi awon gaba da shi.

Wata majiya ta ce DPO ya samu labarin cewa ‘yan bindiga na hari a karamar hukumar Nasarawa Eggon, kuma yayin da yake kokarin kai dauki ne yan bindigar suka sace shi.

Al’ummar yankin sun bayyana CSP Haruna AbdulMalik a matsayin jajirtaccen dan sanda, da ke taka rawa wurin tabbatar da tsaro a Nasarawa-Eggon.

Leave a Reply