By Muhammad Sani Muazu
Hukumar Malaman Jihar Bauchi ta amince da cire shugaban makarantar Government Day Secondary School Kirfi, Malam Musa Ahmed Ningi, da kuma babban malami a makarantar, Malam Adamu Shehu, bisa zargin aikata rashin da’a.
Wata sanarwa da mai rikon babban sakataren a hukumar, Garba Muhammad Bashe, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan sakamakon binciken kwamitin mutum hudu da hukumar ta kafa, wanda ya same su da laifin sayar da kayayyakin makarantar ba bisa ka’ida ba.
Kayayyakin da aka sayar sun hada da gadon dalibai na karfe guda 32 da aka lalata, manyan tukwane na aluminium guda tara, da wani adadi na kwanon rufin saman makarantar (zinc) da ba a tantance yawansu ba.
Hukumar ta kuma amince da sauke su daga mukaminsu, tare da umarnin a tura su zuwa wasu makarantu daban-daban domin ci gaba da koyarwa.
Baya ga haka, hukumar ta umurci jami’an biyu da su dawo da kudin da ya kai naira dubu dari biyar da casa’in da bakwai (N597,000), wanda shi ne kimar kayayyakin da aka lalata. Shugaban makarantar da aka cire, Malam Musa Ahmed Ningi, zai kuma dawo da karin naira dubu saba’in da biyu (N72,000) domin biyan hakkokin ma’aikatan wucin gadi na makarantar.
Hukumar ta kuma jaddada kudirinta na yin aiki tare da hukumomin tsaro domin ganin an dawo da kayayyakin da aka lalata tare da jan kunnen malaman da shugabannin makarantu kan rashin da’a da aikata laifuka a makarantu a fadin jihar.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









