Hukumar EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, kuma ɗan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC.
EFCC ta tasa keyar Rochas daga gidansa da ke unguwar Maitama a babban birnin tarayya Abuja da yammacin Talata.
Jami’an hukumar ta EFCC da hadin gwiwar hukumar ‘ƴan sanda sun yi dirar mikiya tare da mamaye gidan tsohon gwamnan, inda rahotanni suka ce an yi harbi a ƙoƙarin kama shi.
Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan ƙin amsa gayyatar da tsohon gwamnan ya yi bayan tsallake belin da ya samu a farko.
A ranar 24 ga watan Junairun shekarar 2022 ne EFCC ta shigar da kara a gaban kotu tana tuhumar Okorocha da laifuka 17 da suka hada da karkatar da kudaden al’umma da kadarori da kudin su ya kai naira biliyan 2.9.
Hukumar ta kuma kara da cewa yunƙurin gurfanar da Sanata Okorocha a gaban kuliya sau biyu ya ci tura sakamakon ƙin amsa gayyatar da aka yi ma shi.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.