Rabiu Kwankwaso, Éan takarar shugaban kasa a jamâiyyar NNPP, ya ce ba zai bari a lalata harkokin tashoshin ruwa yadda aka saba ba idan aka zabe shi a 2023.
Ya ce Najeriya na bukatar ingantaccen tsari a Éangaren teku domin ta kasance mai matukar muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasar.
Mista Kwankwaso ya kuma yi kira da a gaggauta gyara tare da rage cunkoso a hanyar shiga tashar ruwa ta Apapa a jihar Legas.
Æan takarar shugaban Æasa r na jamâiyyar NNPP ya yi wannan kiran ne a wani taro da masu ruwa da tsaki a harkar ruwa da kamfanin Prime Maritime Project ya shirya a Legas a yau Talata.
A cewar Kwankwaso, lallai kasar nan na bukatar ta tsara yadda za a samu ci gaba a fannin teku domin yana da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma ci gaban tattalin arzikin kasar.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.


