Jamiâan Hukumar Tsaro ta DSS da kuma âyan sanda sun rufe sakatariyar jamâiyyar adawa ta PDP ta Jihar Ondo.
Hukumomin tsaron sun dauki matakin ne a safiyar Litinin a daidai lokacin da alâummar jihar suke gunaguni da neman gwamnatin jihar ta bayyana musu inda Gwamna Rotimi Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki.
Ana zargin hukumomin tsaron sun rufe ofisihin jamâiyyar ne sakamakon shirin wasu âyan jamâiyyar na gudanar da zanga-zanga kan rashin kasancewar gwamnan a jihar na tsawon lokaci.
Da farko Gwamna Akerodule wande ke fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba, ya shafe wata uku a kasar Jamus, inda yake jinya, kafin ya dawo jihar a watan Satumba.
Tun bayan dawowar gwamnan, ya ci gaba da zama a gidansa, da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, lamarin da ya sa babbar jamâiyyar adawa ta PDP a jihar kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa.
A ranar Lahadi PDP ta yi barazanar jagorantar wani gagarumin zanga-zanga a birnin Akure a yau Litinin, domin neman sanin inda Mista Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki da ya hana shi zama a Jihar Ondo.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani kan halin da ake ciki daga kakakin Rundunar âYan Sanda ta Jihar Ondo Funmilayo Odunlami-Omisanya, amma hakar ba ta cim-ma ruwa ba.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









