Home Labarai Kamfanin Air Peace Zai Gana Da Masarautar Kano

Kamfanin Air Peace Zai Gana Da Masarautar Kano

Shugaban kamfanin Air Peace Onyeama ya bayyana Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a matsayin mutum mai son maslaha da zaman lafiyar al’umma, don haka ne ma kamfanin jirgin saman zai yi tattaki zuwa Kano don fayyace wa Masarautar Kano inda gizo ke saka kan zargin da Masarautar tayi na kin girmama Sarki Aminu.

Masauratar tana zargin kamfanin da kin kara lokacin tashin jirgi, jirgin wanda Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya kamata yana cikinshi, amma bai samu shiga ba saboda mahukuntan Air Peace sun ki su kara lokaci da zai zama Sarkin ya iso filin jirgin da tawagarshi.

Onyeama ya bayyana cewa an samun kuskure ne kawai, shiyasa ma kamfaninsa zai yi kokarin ganin ya fayyace wa masauratar yadda lamarin yake. Kuma zai iya kokarinshi wajen nunarwa Masarautar cewa ba nufin kamfanin jirgin bane ya wulakantar Masarautar Kano mai girma.

SourceLeadership Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.