Kotun sauraron kararrakin zaben Sanata mai wakiltar Kogi ta Gabas ta kori, Sanata Jibrin Isah, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da haraji sakamakon soke zabe a wasu rumfunan zabe 94.
Kotun ta kuma umarci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta shirya zabe a rumfunan zabe 94 da abin ya shafa.
Shugaban kotun, Justice K.A. Orjiako, wanda ya yanke hukunci kan karar da Dr Victor Adoji, dan takarar jam’iyyar PDP ya gabatar a gabanta, ya amince da bukatar Adoji.
Adoji, ta bakin Lauyan sa, Mista Johnson Usman (SAN), ya kalubalanci dawowar Jibrin Isah kan hujjar cewa an soke zabe a wasu rumfunan zabe inda katin zabe da aka karba ya zarce tazarar kuri’un da aka ayyana nasarar da ya samu.
Mai shigar da kara ya roki kotun da ta soke zaben Isah tare da bayar da umarnin sake gudanar da zabe a rumfunan zabe 94 da abin ya shafa a mazabar majalisar dattawa.
Da yake zartar da hukuncin, Mai shari’a K.A. Orjiako ya amince da soke nasarar Isah tare da ba da umarnin a janye takardar shaidar cin zabensa.
“Tunda katin zabe da aka tattara a rumfunan zabe 94 ya kai 59,730, yayin da tazarar nasara ita ce kuri’u 26,922, ya kamata jami’in zabe ya bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba ba tare da ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe ba.
“Saboda haka, wannan kotun ta bayar duba bukatsr da masu shigar da kara suka nema.
“Kotu ta kuma umarci INEC da ta gudanar da wani zaben a rumfunan zabe da ba a gudanar da zaben ba ko kuma aka soke zaben don tantance wanda ya yi nasara,” Cewar mai shari’a Orjiako.
Jaridar Leadership
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.