Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa ta Najeriya ta ki amincewa da bukatar yada zaman shariâar ta kafafen yada labarai kai tsaye, kamar yadda masu korafi manyan âyan hamayya suka bukata.
Dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata na 2023 Atiku Abubakar da jamâiyyarsa ta PDP suka bukaci a rika yada shariâar kai tsaye, kamar yadda shi ma dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar Labour tare da jamâiyyar tasa Peter Obi suka gabatar da wannan bukata ga kotun.
A sanarwar hukuncin da kotun ta yi wadda bakin alkalanta biyar ya zo daya ta ce bukatar ba ta da cancanta inda jagoran masu shariâar Justice Haruna Tsammani a bayaninsa ya ce ba wata doka ta Najeriya da ta bayar da damar nuna zaman shariâa ta talabijin saboda haka suka yi watsi da ita.
A bukatar da bangarorin âyan hamayyar suka shigar daban-daban sun nuna cewa nuna shariâar ta talabijin abu ne da ya zama dole saboda shaâawar da jamaâa ke da ita a kai da kuma damuwar da aka nuna a kan sakamakon zabe shugaban kasar na ranar 25 ga watan Fabarairun 2023.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








