Gwamnatin jihar Kwara ta warware basussukan da suka kai naira miliyan 22.5 na kudaden sabunta lasisin gidan rediyon jihar da hukumar kula da kafafen watsa labarai ta kasa NBC ke bin su.
Kwamishinan Sadarwa na Jihar, Bode Towoju, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, ya ba da izinin biyan kudaden ga Hukumar nan take, yana mai lura da cewa bashin nasu ya taru ne tun daga shekara ta 2006.
Ya kuma bayyana cewa tun da farko gwamnatin jihar ta biya naira miliyan 10 daga cikin bashin naira miliyan 32.5 na farko a watan Satumban 2021.
Daga karshe sanarwar ta tabbatar wa mazauna jihar kudurin gwamnati na kawo ci gaba wa jihar da al’ummar ta baki daya.
A makon da ya gabata ne dai hukumar NBC ta kwace lasisin gidajen rediyo da talabijin 52 tare da yin barazanar rufe ayyukansu cikin sa’o’i 24 bisa zargin kin biyan basussukan daya kai Naira biliyan 2.6.
Sai dai daga baya hukumar ta bukaci tashoshin da su biya duk wasu kudaden lasisin da ake biya kafin ranar 23 ga watan Agustan 2022 ko kuma a rufe dukkanin tashoshin karfe 12 na ranar 24 ga watan Agusta.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.