Latest:
LabaraiPolitics

Kwankwaso Ya Naɗa Abdulmumin Kakakin Yaɗa Labaran Famfen Din Sa

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, ya naɗa Abdulmumin Jibrin da Ladipo Johnson Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen.

Naɗin su biyun na cikin wata sanarwar da aka fitar a shafin Tiwita na Kwankwaso.

A bayanan da ya watsa a shafin, taohon Gwamnan Kano ɗin ya amince da naɗa Jibrin da Johnson saboda gogewar su wajen iya ayyukan da ake buƙatar su yi da kuma kuzarin su wajen isar da manufofin NNPP a faɗin ƙasar nan.

“Na amince da naɗa Honorabul Abdulmumin Jibrin da Barista Ladipo Johnson matsayin kakakin yaɗa labarai na rundunar yaƙin neman zaɓe na.

“Ba na ko tantama su biyu ɗin za su yi amfani da ƙwarewa da gogewar da su ke da ita a fagen da ake so su yi aikin da aka ɗora masu, wajen ganin mun cimma nasarar gina Sabuwar Najeriya.” Inji Kwankwaso.

Jibrin dai tsohon Ɗan Majalisar Tarayya ne, kuma ya shiga NNPP cikin watan Mayu, bayan ya samu saɓani da Gwamna Abdullahi Ganduje ne Kano.

Jama’a da dama sun yi mamakin ficewar da daga APC daidai lokacin da ya ke da kusanci da Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.

Idan an tuna, Jibrin ne ya fara tara limamai da malamai a Jihar Kano aka yi wa Tinubu addu’a ta neman nasarar cin zaɓen fidda gwanin APC.

Leave a Reply