Latest:
Labarai

Likitoci Masu Neman Kware Sun Janye Zanga-zangar Da Suka Shirya

Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Nijeriya, ta dakatar da zanga-zangar da ta shirya yi a duk fadin kasar nan bayan wata ganawar sirri da ta yi da manyan jami’an majalisar dattawa.

Shugaban NARD, Emeka Orji ne ya bayyana haka a zantawarsa da manema labarai.

Orji, duk da haka, ya ce za su yi nazari cikin sa’o’i 72 masu zuwa.

“Mun gana da shugaban majalisar dattawa, shugabannin masu rinjaye da marasa rinjaye. Don haka, an dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi ranar Laraba kuma za mu sake duba nan da sa’o’i 72.”

Likitocin da ke yajin aiki tun da farko sun shirya fara zanga-zangar lumana a kowace rana, daga ranar Laraba, idan gwamnati ta gaza biyan bukatunta.

Matakin dai ya biyo bayan umarnin da gwamnatin tarayya ta ba manyan daraktocin kula da lafiya na manyan asibitocin gwamnatin tarayya da su fara aiwatar da manufar “idan ba aiki, babu albashi” a kan likitocin da ke yajin aikin.

A ranar 26 ga watan Yuli ne likitocin suka fara yajin aiki, biyo bayan gazawar gwamnati wajen biyan bukatunsu.

Likitocin suna neman aiwatar da manufar karin albashi ga ma’aikatan kiwon lafiya da kuma wasu sauran bukatunsu.

Jaridar Leadership

Leave a Reply