Home Labarai Lauyoyi A kasar Burtaniya Na Yajin Aiki Sabida Karancin Albashi

Lauyoyi A kasar Burtaniya Na Yajin Aiki Sabida Karancin Albashi

Lauyoyi na yajin aiki a Burtaniya kan batun ƙarancin albashi da aka jima ana dambarwa a kai.

Lauyoyin sun fice daga kotunan ana tsaka da gudanar da shari’o’i a sassa daban-daban na ƙasar.

Hakan ya dakatar da shari’o’i 8 cikin 10 da ake yi a wata kotu da ke Old Bailey a Landan.

Sakatarin harkokin shari’a, Dominic Raab ya ce yajin aiki zai jinkirta shari’o’i, adaidai lokacin da kotunan ke fama da yawan shari’o’i da ake jira a yanke hukunci kusan dubu 58.

Lauyoyin sun yi watsi da batun karin kashi 15 cikin 100, kuma za su dau matakin da ya zarce wannan nan da mako hudu gaba.

Kungiyar lauyoyi ta kasar Burtaniya ta nemi anyi musu karin akalla kashi 25 cikin 100 na matsakaicin albashinsu.

Wannan matsala da ake fuskanta ta sanya lauyoyi 300 barin aikinsu a shekarar da ta gabata.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.