Labarai

Naira Biliyan 187 Tayi Kadan Wa Aikin Kidaya A Najeriya – NPC

Hukumar Kidiya ta kasa ta sanar da cewa biliyan 187 da aka ware a kasafin kudi don kirga al’umma da gidaje, da aka shirya yi a watan Afrilun 2023.

Shugabar hukumar ta riko Ugoeze Mbagou ce ta sanar da hakan ranar Alhamis, a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.

An sake tada batun sake kidaya a Najeriya a karon farko bayan shekaru 17 da aka yi irinsa a 2006, wanda hakan ya saba shawarar Majalisar Dinkin Duniya da ta shata tazarar shekara 10.

Jaridun cikin gida sun ambaro Mbagou na cewa gudanar da kidaya a babbar kasa kamar Najeriya na bukatar kudin da ya haura naira biliyan 187.

Akan haka ta bukaci a sake duba kasafin kudin don duba yiwuwar kara wani abu.

Sai dai kuma ta ce rabin kudin kidayar zai fito ne daga kungiyoyin da ke bada tallafi ta wannan haujin.

Leave a Reply