Kungiyar Likitoci ta Nijeriya (NARD), a daren ranar Talata, ta sanar da fara yajin aikin sai baba-ta-gani, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnati wajen biyan bukatun mambobinta.
Shugaban NARD, Dokta Emeka Orji, ya shaida wa wakilinmu cewa yajin aikin ya fara ne da safiyar Laraba 26 ga watan Yuli, 2023.
Ya ce an cimma matsayar ne a taron da mambobinta suka gudanar a ranar Talata a Legas.
Orji, ya ce bukatunsu sun hada da karin albashin kashi 200 cikin 100, maye gurbin likitocin da suka yi murabus da biyan alawus na horarwa na 2023.
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya gana da shugabannin kungiyar NARD a ranar Litinin, inda ya roke su da su ba shi makonni biyu don ganawa da Shugaban kasa Bola Tinubu kan bukatun kungiyar.
Jaridar Leadership
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.