Labarai

An Kama Wani Mutum na yunkurin yin fyade wa tsohuwar matarsa

 

Dubun wani mutum mai shekara 47 ta cika a yayin da ya yi yunkurin yin fyade ga tsohuwar matarsa.

’Yan sanda sun gurfanar da shi ne a gaban kotun majistare da ke yankin Ogba a Jihar Legas, bayan tsohuwar matar tasa ta kai kararsa a caji ofis.

Dan sanda mai gabatar da kara, Akinleye Funmilola ya shaida wa alkali O.O. Hughes cewa wanda ake kara ya fake ne da neman sasantawa da tsohuwar matar tasa, inda ya yi amfani da damar ya je gidanta, amma ya nemi zakke mata da karfin tuwo.

A kan haka ne tsohuwar matar tasa ta yi kururuwar neman agaji, har makwabta suka kawo mata dauki suka ritsa shi, a kai shi ofishin ’yan sandan yankin.

Akinleye ya ce da farko wata kotu ce ta raba auren tsoffin ma’uratan saboda yawan rikice-rikice da kuma fada da juna a tsakaninsu.

Hakan ne ya sa a lokacin matar ta nemi kotu ta raba auren nasu, duk kuwa da cewa Allah Ya albarkace su da samun ’ya’ya, wanda bayan sauraron kowane bangare aka raba auren, kowannensu ya kama gabansa.

Daga bisani tsohon mijin nata ya dawo yana neman su sasanta ta dawo wurinsa, amma a garin haka ya nemi ya yi mata fyade.

Sai dai wanda ake tuhumar ya musanya zargin, inda kotun ta ba da belinsa a kan N10,000 ta kuma dage sauraron karar.
(Jaridar Aminiya)

Leave a Reply