Gwamnatin jihar Gombe ta amince da yi wa ma’aikatan jihar ƙarin naira 10,000 a albashinsu, a wani ɓangare na rage raɗadin cire tallafin man fetur.
Yayin da yake jawani ga manema labarai a birnin Gombe, mataimakin gwamnan jihar Dakta Manasseh Daniel Jatau ya ce ƙarin albashin na daga cikin matakan da gwamnan jihar Muhammadu Inuwa Yahaya ke ɓullowa da su domin rage wa ‘yan jihar raɗaɗin da suke ciki sakamakon cire tallafin man fetur.
Ya kara da cewa tun bayan cire tallafin man fetur gwamnatin jihar ke ɗaukar matakai domin tallafa wa ‘yan jihar ta hanyar raba kayan tallafi ga mutum 30,000.
Mataimakin gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar da na burin raba kayan tallafin ga mutum aƙalla 420,000 a faɗin jihar.
Dakta Jatau ya ce karin naira 10,000 da aka kara wa ma’aikatan ya shafi duka ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi a jihar, kuma karin ya fara ne daga watan Agusta.
Da aka tambaye shi zuwa wane lokaci za a ɗauka ana biyan ƙarin albashin, sai ya ce kawo yanzu babu iyaka.
Tun bayan cire tallafin man fetur ɗin ne gwamnatocin jihohin ƙasar, suka riƙa ɓullo da matakai daban-daban da nufin rage wa ma’aikatansu wahalhalun da suke fuskanta.
Inda wasu jihohin suka rage kwanakin aiki daga biyar zuwa uku ga ma’aikatan nasu.
Kungiyoyin ƙwadagon ƙasar na ta kiraye-kiyaren yi wa ma’aikata ƙarin albashi sakamakon wahalhalun da ma’aikata ke fuskanta sakamkon cire tallafin man fetur din.
BBC Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.