Home Labarai Masu aikin ceto sun gano daruruwan gawarwaki a gabar Tekun Libya

Masu aikin ceto sun gano daruruwan gawarwaki a gabar Tekun Libya

 

Masu aikin ceto na kasar Malta sun ce sun gano daruruwan gawarwaki a gabar teku a birnin Derna na Libiya a ranar Juma’a.

Kungiyar Malta Civil Protection Deparment a ranar Asabar ta bayyana cewa kusan gawarwaki 400 suka gano bayan ambaliyar ruwan da ta yi sanadin mutuwar dubban mutane a Libiya.

“Akwai watakila kusan gawarwaki 400, amma da wahala bayyanawa,” in ji Natalino Bezzina, wanda ke jagorantar tawagar masu aikin ceto na kasar Malta a tattaunawarsa da jaridar kasar Malta.

Kasar ta Malta ta aika da masu aikin ceto 72 daga cikin rundunar sojinsu da kuma ta kare farar hula a ranar Laraba.

Mutum hudu daga cikin tawagar ne suka soma gano gawarwakin inda suka soma gano gawarwaki bakwai a cikin wani kogo da ke gefen teku, cikin gawarwakin har da na yara uku.

Ana zaton ruwa ne ya jawo gawarwakin sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi wanda ya jawo ambaliya, lamarin da ya sa har madatsun ruwa biyu suka fashe a ranar Lahadi.

Bezzina ya shaida wa kafafen watsa labarai na Malta cewa wani dan karamin rukuni na masu ceto ya je kusa da kogon wanda ruwa ya shanye rabinsa inda suka gano gawarwaki a ciki.

A daidai lokacin da suke ci gaba da neman gawarwakin, sai ma’aikatan Libiya suka taya su aikin inda daga nan ne suka ga daruruwan gawarwaki.

TRT Afrika Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.